Kamfanin dillancin labaran Sharq Ausat na kasar Masar ya habarta cewa, tun daga ranar Asabar da ta gabata ce aka fara barin wuta a birnin Benghazi, tsakanin tsoffin 'yan tawayen kasar da ke dauke da makamai da kuma sojoji, rahoton ya ce tun daga daren jiya har zuwa asubahin yau ana jin barin wuta, kuma majiyoyin asibiti sun tabbatar da mutuwar fiye da mutane 40.
Rikicin baya-bayan nan a kasar Libya ne ya fara ne kasa da makonni biyu da suka gabata, bayan da tsoffin 'yan tawayen kasar daga yankin Misrata suka kaddamar da farmaki kan filin safkar jirage na Tripoli da nufin kwace iko da shi daga hannun 'yan tawaye na Zantan, lamarin da ya yi sanadiyyar konewar jirage da dama tare da kashe mutane fiye da 50.
Yanzu haka dai kasashen duniya da dama sun rofe ofisoshin jakadancinsu tare da janye jakadunsu daga kasar ta Libya har sai abin da hali ya yi, domin kauce wa yakin da ake yi a kasar. ABNA